Labarai
Gobara ta kama tashar mai a Abuja
Gobara ta kama wani gidan mai da ke Abuja, babban birnin Najeriya a ranar Juma’a.
Tashar man fetur ta Enyo da ke shiyya ta daya a yankin Wuse a babban birnin tarayyar Najeriya ta tashi da wuta da misalin karfe 7:00 na dare agogon Najeriya.
Mazauna yankin sun ce sun fara jin karar fashewar wani abu mai karfi kafin su ga gobarar ta ci.
Wani ganau ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa gobarar ta tashi ne daga wata tankar mai da aka ajiye a cikin gidan mai.
“Ta tashi daga tankar mai ta kuma bazu zuwa ga dukkan motocin da aka ajiye a wurin,” in ji shaidar, ya ki bayyana sunansa.
Gobarar na ci gaba da tashi a lokacin da aka kawo rahoton. Sai dai tun da farko mutanen da suka fusata sun fatattake su bisa zargin sun zo a makare, yanzu haka ma’aikatan kashe gobara na fafatawa don kashe wutar.
Goyon bayan PREMIUM TIMES ta aikin jarida na gaskiya da rikon amana Aikin jarida yana kashe makudan kudade. Amma duk da haka aikin jarida mai kyau ne kawai zai iya tabbatar da yuwuwar samar da al’umma ta gari, dimokuradiyya mai cike da gaskiya, da gwamnati mai gaskiya. Don ci gaba da samun damar samun mafi kyawun aikin jarida na bincike a cikin ƙasa muna rokon ku da ku yi la’akari da bayar da tallafi kaɗan ga wannan kyakkyawan aiki. Ta hanyar ba da gudummawa ga PREMIUM TIMES, kuna taimakawa don dorewar aikin jarida mai dacewa da kuma tabbatar da cewa ya kasance kyauta kuma yana samuwa ga kowa.
Ba da gudummawa
RUBUTU AD: Kira Willie – +2348098788999