Duniya
EFCC ta kama daraktan asusu na NCAA, da wasu mutane 3 bisa zargin damfarar N2bn ‘DTA’
Jami’an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC sun cafke wasu manyan jami’an hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya NCAA guda hudu.
A cewar rahoton PRNigeria, an damke jami’an hukumar ta NCAA bisa zargin damfarar N2bn Duty Tour Allowance, DTA, a hukumar.
Wadanda ake zargin sun hada da: Bilkisu Adamu Sani, darakta a kudi da asusu; Hart Benson Fimienye, mataimakin babban manaja, Treasury; Obene Jenbarimiema Turniel, mataimakin babban manaja (Asusun Gudanarwa) da Nathaniel Terna Kaainjo, babban manajan (Accounts and Stores).
Wata majiya mai tushe ta shaida wa PRNigeria cewa an kai Mista Nathaniel a hannun EFCC a ranar Alhamis, 16 ga watan Maris, yayin da sauran kuma aka kama su a ranar Litinin, 20 ga watan Maris.
A cewar majiyar, tawagar jami’an tsaro na ci gaba da gasa wadanda ake zargin a hedikwatar hukumar da ke Abuja.
Credit: https://dailynigerian.com/efcc-arrests-ncaa-account/