Direba ya kashe dan jaridan Vanguard – ‘Yan sanda

0
12

Wani direban mota ya kashe dan jaridar Vanguard Tordue Henry-Salem da ya bata a ranar Alhamis, kamar yadda hukumomin ‘yan sanda suka bayyana.

Kakakin rundunar, Frank Mba ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a yayin da yake gabatar da direban da ya kashe dan jaridan a ofishin ‘yan sanda na rundunar ‘yan sanda, IRT, harabar Guzape, Abuja.

A rahoton da jaridar The Nation ta wallafa, an gano gawar Mista Salem ne a babban asibitin Wuse.

Short Link: https://nnn.ng/hausa/?p=27463