Connect with us

Kanun Labarai

Daliban FGC Yauri 30 sun sake samun ‘yanci bayan shafe watanni 7 a hannunsu

Published

on

  Gwamnatin jihar Kebbi ta ce dalibai 30 da wani malamin kwalejin gwamnatin tarayya FGC Birnin Yauri da wasu yan bindiga suka sace a watan Yunin bara sun sami yanci Yahaya Sarki mai magana da yawun gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya rabawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya a Birnin Kebbi ranar Asabar Mista Sarki ya ce A yau Asabar 8 ga watan Janairu 2022 dalibai 30 na Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Yauri da malami daya sun isa Birnin Kebbi babban birnin Jihar Kebbi bayan an sako su Za a yi musu gwajin lafiya tare da tallafa musu yayin da ake sake haduwa da iyalansu Muna godiya ga dukkan hukumomin tsaro da wadanda suka taimaka wajen ganin an sako mutanen yayin da muke taya Shugaba Muhammadu Buhari murnar nasarar da aka samu NAN ta tuna cewa an sako daliban makarantar guda 30 ne a ranar 21 ga Oktoba 2022 aka kawo su Birnin Kebbi suka koma da iyalansu Wannan baya ga wasu da aka sake su a baya ga iyayensu NAN
Daliban FGC Yauri 30 sun sake samun ‘yanci bayan shafe watanni 7 a hannunsu

Gwamnatin jihar Kebbi ta ce dalibai 30 da wani malamin kwalejin gwamnatin tarayya, FGC Birnin Yauri, da wasu ‘yan bindiga suka sace a watan Yunin bara, sun sami ‘yanci.

Yahaya Sarki, mai magana da yawun gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya rabawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya a Birnin Kebbi ranar Asabar.

Mista Sarki ya ce: “A yau Asabar 8 ga watan Janairu, 2022 dalibai 30 na Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Yauri, da malami daya sun isa Birnin Kebbi, babban birnin Jihar Kebbi, bayan an sako su.

“Za a yi musu gwajin lafiya tare da tallafa musu yayin da ake sake haduwa da iyalansu.

“Muna godiya ga dukkan hukumomin tsaro da wadanda suka taimaka wajen ganin an sako mutanen, yayin da muke taya Shugaba Muhammadu Buhari murnar nasarar da aka samu.”

NAN ta tuna cewa an sako daliban makarantar guda 30 ne a ranar 21 ga Oktoba, 2022, aka kawo su Birnin Kebbi suka koma da iyalansu.

Wannan baya ga wasu da aka sake su a baya ga iyayensu.

NAN