Boko Haram ce ke da alhakin kai hare-hare kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna – Majiyar leken asiri

0
12

Hare-haren baya-bayan nan kan matafiya a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna, kungiyar Boko Haram ce ta kai su, kamar yadda jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito.

A ranar Lahadin da ta gabata ne ‘yan ta’addan suka yi awon gaba da wasu fasinjoji da ba a tantance adadinsu ba tare da kashe wani fitaccen dan siyasar Zamfara mai suna Sagir Hamidu, a inda ake kira Kurmin Kare a kan babbar hanyar.

Washegari ‘yan ta’addan suka dawo kusa da wuri guda, kuma kusan lokaci guda suka bude wuta kan matafiya tare da sace wasu da dama.

Sai dai wata majiyar leken asiri a Abuja ta shaidawa jaridar DAILY NIGERIAN bisa sharadin sakaya sunanta cewa ‘yan ta’addar Boko Haram ne suka kai hare-haren na baya-bayan nan, inda a yanzu haka suke kafa sansani a dazuzzukan Kaduna da Nijar.

“Bisa ga jami’an tsaro da aka kama, ‘yan ta’addan Boko Haram ne suka kai wadannan hare-hare na baya-bayan nan a yankin Kurmin Kare da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

“Su ne kuma suke yin garkuwa da mutane a kusa da Mashegu da Shiroro a Jihar Neja. Suna ƙoƙarin kafa kansu a kewayen yankin, don haka suka shiga yin garkuwa da su don samun kuɗin kayan aiki.

“Kun san an yi musu ruwan bama-bamai a yankunan su a Birnin Gwari da Giwa da Chikun da Igabi da dai sauransu. Don haka bayan sun gudu daga wadannan wurare, yanzu sun yada zango a wasu wuraren da bai wuce kilomita 50 zuwa 60 ba daga babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.

“Daga wadannan wuraren, suna amfani da babura don tafiya. Akwai rafi da ke gefen hanyar inda suke ajiye baburan kuma suna tafiya da kafa ta cikin wani dajin mai kauri domin kai hare-haren,” inji majiyar.

A cewarsa, an sanar da hukumomin tsaro da kuma gwamnatocin jihohin Neja da Kaduna game da ci gaban da ake yi da kuma kokarin lalata su.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, Mohammed Jalige, bai samu jin ta bakinsa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Short Link: https://nnn.ng/hausa/?p=28323