Duniya
An kai harin bam a Kabul babban birnin Afganistan
Kakakin ‘yan sandan Kabul Khalid Zadran ya bayyana cewa, wani harin bam da aka kai a Kabul babban birnin kasar Afganistan a ranar Laraba ya janyo hasarar rayuka.
“An kai wani bam a kan hanyar da ta kai ma’aikatar harkokin wajen kasar da misalin karfe 04:00 na yamma agogon kasar amma abin takaici ya haddasa asarar rayuka,” in ji Zadran.
Jami’in ya ce za a raba cikakken bayani ga manema labarai daga baya.
Hanyar da ta nufi ma’aikatar harkokin wajen ta ratsa kantunan kasuwanci da dama da hukumomin gwamnati da suka hada da gidan Firayim Minista da cibiyar yada labarai ta gwamnati.
Babu wata kungiya ko wani da ya dauki alhakin fashewar.
Xinhua/NAN
Credit: https://dailynigerian.com/bomb-blast-leaves-casualties/