Wata matar aure mai juna biyu na wata takwas, Halima Yusuf, don shigar da karar neman tabbatar da saki a Kotun Koli ta Shari’ar Musulunci da ke Mararaba a Jihar Nasarawa.
Halima Yusuf ta zargi mijinta, Isah, da dukanta. A cikin takardar karar da ta shigar, ta kuma zargi mijin nata da yin watsi da nauyin da ke kansa.
“Mun yi aure ne a karkashin Shari’ar Musulunci. Isah ba ya samar min da abinci, tufa, ko kula da lafiyata,” in ji ta.
Mai shigar da karar ta shaida wa kotun cewa, tana da juna biyu na wata takwas, kuma tuni ta koma da zama gidan iyayenta da ke Mararaba.
Ta roki kotun da ta tabbatar mata da sakin, sannan ta bayar da umurnin tilasta wa Isah ya dauki nauyin juna biyun da ke jikinta.
Alkalin kotun, Mohammed Yakubu, ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 11 ga watan Yuni domin ci gaba da sauraron karar.